The news is by your side.

Abin Da Yai Sanadin Rasuwar Jigo A ADC Daga Jigawa Da Ƴan Bindiga Suka Kama

69

Tsohon ɗan majalisar wakilai daga Jihar Jigawa, Abba Anas Adamu, ya rasu bayan shafe kwanaki a hannun ƴan bindiga da suka yi garkuwa da shi.

An sace Abba Anas ne a ranar Larabar da ta gabata a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Marigayin, wanda jigo ne a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya wakilci mazaɓar Guri, Kiri-Kasamma da Birniwa a majalisar wakilai tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.

Rahotanni sun ce yana kan hanyarsa daga Kano zuwa Abuja domin halartar wani taron siyasa lokacin da lamarin ya faru.

An yi garkuwa da shi ne tare da wani abokinsa mai suna Ali Tukur Gantsa, inda aka ce masu garkuwar sun kai su cikin daji kusa da Jere tare da neman kuɗin fansa na naira miliyan 200.

Mazauna yankin sun ce bayan doguwar tattaunawa, masu garkuwar sun amince da karɓar naira miliyan 50.

Rahotannin sun nuna cewa bayan biyan kuɗin, an saki Gantsa, amma Abba Anas bai tsira ba.

An bayyana cewa marigayin na fama da cutar asma da ta hawan jini.

Mazauna yankin sun ce an tsare shi ba tare da samun magungunansa ba na tsawon kwanaki, lamarin da ya ƙara taɓarɓarewar lafiyarsa har ya rasu.

Jigo a jam’iyyar ADC, Sabo Muhammad Nakudu, ya tabbatar da rasuwar a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin da rana.

“Ina miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayi Abba Anas Adamu wanda ƴan bindiga suka kashe bayan tsare shi na kwanaki. Ina roƙon Allah ya jiƙansa ya sanya shi a Aljannatul Firdausi,” in ji Nakudu.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam, ya ce har yanzu ba a kai masa cikakken bayani kan lamarin ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.