The news is by your side.

Ƴar Ekiti Na Kan Gaba A Jerin Ɗalibai 10 Da Suka Fi Cin Jarabawar JAMB Ta 2026

48

Owoeye Daniella Jesudunsin daga jihar Ekiti ta zama dalibar da ta fi kowa samun maki a jarabawar shiga manyan makarantu ta shekarar 2026 (UTME) da Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta gudanar, bayan ta samu maki 372 cikin 400.

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron tsara manufofin ɗaukar ɗalibai na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Rahoton TheCable ya ce Jesudunsin ta rubuta jarabawar ne a jihar Ogun, inda kuma ta zaɓi Jami’ar Legas (UNILAG) a matsayin makarantar da take son shiga domin karantar fannin likitanci da tiyata.

Oloyede ya ce makin nata ya gaza da maki uku kacal idan aka kwatanta da mafi girman makin shekarar 2025, wanda Chinedu Okeke daga jihar Anambra ya samu da maki 375.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Enwere Kingsley Ikenna daga jihar Imo ne ya zo na biyu da maki 370 bayan rubuta jarabawar a Jihar Legas.

Ikenna ya zaɓi Nile University da ke Abuja domin karantar fannin Kimiyyar Kwamfuta.

Sai kuma Bamisile Ayomide Emmanuel daga jihar Ondo wanda ya zo na uku da maki 369, inda ya zaɓi Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure (FUTA) domin karantar Software Engineering.

Sauran ɗaliban da suka samu manyan maki sun haɗa da Olabiyisi Olanrewaju Oluwatimileyin daga jihar Oyo, Victor-Onyeka Daniel Ifeanyi daga Imo, Osagiobare Daniel Osahenrumwen daga Edo, Ademiluyi Adebowale Anthony daga Osun da kuma Azuike Kenechukwu Anthony daga Anambra, waɗanda dukkansu suka samu maki 368.

Haka kuma Offorkile Michael Okechukwu daga jihar Abia, Adebisi Eniola Sonari daga Ogun da Umukoro Gift Orhenevovwero daga Delta sun samu maki 367.

A yayin taron, Oloyede ya sanar da cewa JAMB za ta fara bai wa ɗalibai damar amfani da na’urorinsu wajen rubuta jarabawar UTME daga shekarar 2027.

Ya ce tsarin “Bring Your Own Device” zai bai wa ɗalibai damar amfani da kwamfutocinsu ko wasu na’urori, inda za a saka wata na’ura ta musamman domin hana maguɗin jarabawa.

A cewarsa, sabon tsarin zai rage kuɗin gudanarwa tare da sauƙaƙa aikin shirya jarabawar, sannan zai rage ƙorafe-ƙorafen ɗaliban da ke cewa kwamfutocin cibiyoyin jarabawa na ɗauke musu yayin rubuta jarabawa.

Oloyede ya ƙara da cewa hukumar za ta ɓullo da wasu sabbin tsare-tsare kafin shekarar 2027 domin inganta gudanar da jarabawar.

Masu ruwa da tsaki a taron sun kuma amince da jadawalin kammala ɗaukar ɗaliban shekarar 2026 a manyan makarantu.

Sun yanke shawarar cewa jami’o’in gwamnati su kammala ɗaukar ɗalibai kafin ko zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2026, yayin da jami’o’i masu zaman kansu za su kammala kafin ranar 30 ga Nuwamba, 2026.

Haka kuma an buƙaci kwalejojin kimiyya da fasaha, monotechnics da kwalejojin ilimi su kammala ɗaukar ɗalibai kafin ranar 31 ga Disamba, 2026.

Oloyede ya gargaɗi dukkan cibiyoyin ilimi da su bi wa’adin da aka gindaya, yana mai cewa duk makarantar da ta gaza kammala ɗaukar ɗalibai a kan lokaci ba za ta sake samun damar ɗaukar ɗalibai a zangon karatun ba.

Ya kuma amince cewa duk ɗalibin da aka ba gurbin karatu dole ne ya amince da shi cikin makonni huɗu, in ba haka ba za a soke gurbin nasa.

A cewarsa, manufar tsarin ita ce tabbatar da adalci, gaskiya da kuma kammala ɗaukar ɗalibai a kan lokaci a dukkan manyan makarantu a Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.