INEC Za Ta Ɗau NYSC Miliyan 1 Da Kusan Rabi Don Aikin Zaɓen 2027
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar za ta tura fiye da ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 domin gudanar da babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.
Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai hedkwatar NYSC da ke Abuja tare da manyan jami’an hukumar zaɓe.
Sanarwar da INEC ta fitar ranar Litinin ta ce Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ne ya tarɓi tawagar a Yakubu Gowon House da ke Abuja.
Shugaban INEC ya ce ƴan bautar ƙasa sun kasance ginshiƙi wajen gudanar da zaɓe a Najeriya tun daga shekarar 1999, musamman a matsayin jami’an rumfunan zaɓe da jami’an yankunan yin rajista.
A cewarsa, a zaɓen shekarar 2023 hukumar ta tura kimanin ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.2, inda sama da mutum 850,000 daga cikinsu suka kasance ƴan bautar ƙasa da masu aikin sa kai daga jami’o’i.
Amupitan ya ce za a buƙaci ƴan bautar ƙasa 707,384 domin zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya ranar 16 ga Janairun 2027.
Ya ƙara da cewa za a sake buƙatar mutum 707,384 domin zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi ranar 6 ga Fabrairun 2027.
Shugaban INEC ya yabawa ƴan bautar ƙasar kan kishin ƙasa da nuna ƙwarewarsu wajen amfani da na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS a rumfunan zaɓe 176,846 a faɗin ƙasar.
Ya kuma tabbatar wa shugabannin NYSC cewa hukumar za ta inganta tsarin inshora, tsaro da walwalar ƴan bautar ƙasa da ake turawa ayyukan zaɓe.
Da yake mayar da martani, Olakunle Nafiu ya ce NYSC za ta ci gaba da tallafawa INEC domin tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe a Najeriya.