Starmer Na Fuskantar Matsin Lambar Ya Sauƙa Bayan Jam’iyyarsa Ta Samu Mummunan Sakamakon Zaɓen
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, na ci gaba da fuskantar kiraye-kirayen yin murabus daga wasu ƴan jam’iyyarsa ta Labour bayan mummunan sakamakon zaɓukan cikin gida da aka gudanar a makon da ya gabata.
Ministoci uku a gwamnatinsa, ciki har da Jess Phillips, sun yi murabus daga muƙamansu yayin da fiye da ƴan majalisar Labour 80 suka buƙaci ya sauƙa daga shugabanci.
A taron majalisar ministoci na mako-mako da aka gudanar ranar Talata a Downing Street, Starmer ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin murabus kuma ya ƙalubalanci duk mai son jagorancin jam’iyyar ya fito fili.
Dokokin jam’iyyar Labour sun tanadi cewa duk wanda zai ƙalubalanci shugaban jam’iyyar dole ne ya samu goyon bayan aƙalla ƴan majalisa 81, daidai da kaso 20 cikin ɗari na ƴan majalisar Labour.
Bayan taron, Sakataren Gidaje Steve Reed da Sakataren Harkokin Aiki da Fansho Pat McFadden sun tabbatar da cewa suna ci gaba da mara wa Starmer baya.
Sai dai Ministan Lafiya, Wes Streeting, wanda ake gani a matsayin mai yiwuwar neman shugabancin jam’iyyar, bai yi magana da manema labarai ba yayin da yake barin fadar Downing Street.
Ministar Harkokin Waje, Jenny Chapman, ta amince cewa ana tattaunawa kan makomar shugabancin Starmer, amma ta ce babu wani minista da ya ƙalubalance shi kai tsaye a taron.
Rahotanni sun nuna cewa ministoci Alex Davies-Jones da Miatta Fahnbulleh ma sun yi murabus daga gwamnati.
Tashin hankalin cikin jam’iyyar ya biyo bayan rashin nasarar jam’iyyar Labour a zaɓukan ƙananan hukumomi a Ingila, inda jam’iyyar ta rasa kusan kujerun kansiloli 1,500.
Jam’iyyar ta kuma rasa mulki a Wales tare da samun mafi muni sakamako a tarihinta a zaɓen majalisar Scotland.
Masu sharhi na ganin rikicin ya ƙara tsananta ne bayan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan naɗin Peter Mandelson a matsayin jakadan Birtaniya a Amurka, matakin da wasu an majalisar Labour suka ce ya jefa shakku kan hukuncin Starmer.