The news is by your side.

Iran Ta Yi Watsi da Ƙudurin Amurka a Kwamitin Tsaro Kan Rikicin Mashigin Hormuz

25

Iran ta yi watsi da wani daftarin ƙuduri da Amurka da ƙawayenta suka gabatar a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kan rikicin Mashigin Hormuz, tana mai bayyana shi a matsayin mai cike da son zuciya da siyasa.

Rahoton jaridar The Times of India ya ce Tehran ta bayyana cewa ƙudurin ba zai warware rikicin da ke ci gaba a yankin Yammacin Asiya ba, tana mai zargin Washington da ƙoƙarin halasta wasu ayyuka da ta kira da ba na bin doka ba ta hanyar Majalisar Ɗinkin Duniya.

A cikin wata sanarwa, Iran ta ce mafita guda ɗaya tilo ita ce kawo ƙarshen yaƙi, ɗage takunkumin ruwa da aka ƙaƙaba wa tashoshin jiragen ruwanta, da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa yadda aka saba a Mashigin Hormuz.

Iran ta kuma yi kira ga ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da su yi watsi da ƙudurin tare da guje wa mara masa baya.

Amurka ce ta gabatar da ƙudurin tare da haɗin gwiwar wasu ƙasashen Gulf da suka haɗa da Bahrain, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait da Qatar.

Ƙudurin na neman kare ƴancin zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigin Hormuz, wanda ke daga cikin manyan hanyoyin jigilar makamashi a duniya da kaso mai yawa na man fetur ke bi ta cikinsa.

Amurka ta zargi Iran da kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci, dasa nakiyoyi a teku da kuma barazana ga zirga-zirgar ruwa.

Rahoton ya ce rikicin ya ƙara haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin bayan samun rahotannin hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa, da kuma tashin hankali da ya shafi Isra’ila.

Sojojin Isra’ila sun ce an ji ƙararrawar tsaro a arewacin ƙasar bayan wani zargi na kutsen jirgin sama.

Rundunar Revolutionary Guard ta Iran ta yi gargaɗi kan duk wani matakin soji, tana mai cewa yunƙurin shugaban Amurka Donald Trump na raunana Tehran ya gaza.

Sai dai rahoton ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawar diflomasiyya, inda masu shiga tsakani ke ƙoƙarin samar da yarjejeniya tsakanin Washington da Tehran.

Rikicin ya haddasa tashin farashin mai da kuma ƙarin kuɗin jigilar kaya a duniya, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar tangarɗa ga kasuwancin duniya da tsaron yankin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.