The news is by your side.

Mutane Shida Sun Rasa Ransu, Wasu Sun Jikkata A Fashewar Bam A Zamfara

49

Aƙalla mutum shida sun mutu yayin da wasu shida suka jikkata sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a gefen hanya a hanyar Bagega zuwa Anka da ke karamar hukumar Anka a Jihar Zamfara.

Rahoton Channels Television ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Alhamis lokacin da wata motar kasuwanci da ke ɗauke da fasinjoji ta taka abin fashewar.

Mazauna yankin sun ce fashewar ta yi mummunar ɓarna ga motar.

Majiyoyin yankin sun zargi wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne da dasa bam ɗin a hanyar.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya tabbatar wa Channels Television faruwar lamarin ta wayar tarho.

Ya ce mutanen shida da suka jikkata na samun kulawa a asibiti sakamakon raunuka daban-daban da suka samu.

Abubakar ya ce rundunar ta tura tawagar masu kula da abubuwan fashewa ta EOD zuwa wurin domin tabbatar da tsaron yankin da hana sake samun asarar rayuka.

A cewarsa, jami’an EOD sun gudanar da bincike a duk hanyar domin gano ko akwai wasu abubuwan fashewa kafin a sake buɗe hanyar ga jama’a.

“An dawo da zaman lafiya a yankin, kuma tawagar EOD ta gudanar da bincike a faɗin wurin domin tabbatar da cewa babu sauran abubuwan fashewa,” in ji shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.