The news is by your side.

Sabon jakadan Najeriya a Birtaniya Aminu Dalhatu ya miƙa takardar shaidar kama aikinsa ga Sarki Charles III

48

Jakadan Najeriya a Ƙasar Birtaniya, Aminu Dalhatu, ya miƙa takardar shaidar wakilcinsa ga Sarki Charles III a Fadar St James’s da ke birnin Landan a ranar Laraba, inda hakan ya ƙaddamar da aikin sa a matsayin babban wakilin diflomasiyyar Najeriya a ƙasar.

Miƙa takardar shaidar wakilcin ya tabbatar da fara aikinsa a hukumance a Birtaniya, wanda ke daga cikin manyan muƙaman diflomasiyya da Najeriya ke da su a ƙasashen waje.

Dalhatu ya kasance tare da matarsa Yasmin da manyan jami’an ofishin jakadancin Najeriya a lokacin da aka gudanar da taron a fadar.

A cewar wata sanarwa da ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya ya fitar a ranar Alhamis, Dalhatu ya isar da gaisuwar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga Sarki Charles III da kuma gwamnatin Birtaniya.

Sanarwar ta bayyana cewa jakadan ya kuma jaddada aniyar Najeriya ta ci gaba da ƙarfafa dangantaka da haɗin gwiwa mai ɗorewa tsakanin Najeriya da Birtaniya a fannoni daban-daban na moriyar juna.

Dalhatu, wanda ya fito daga Jihar Jigawa, ya taɓa riƙe muƙamin jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu kafin wannan naɗin nasa.

Rahotanni sun nuna cewa ya kuma yi aiki a fannoni daban-daban a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya kafin wannan sabon muƙami.

Majalisar Dattawan Najeriya ce ta amince da shi a matsayin ɗaya daga cikin rukunin farko na waɗanda aka tantance domin aikin jakadanci a ƙasashen waje.

Ƙungiyar Nigeria-British Chamber of Commerce ta taya Dalhatu murna kan fara aikinsa a matsayin babban jami’in diflomasiyyar Najeriya a Birtaniya.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ya samu muƙamin ne a wani muhimmin lokaci a dangantakar Birtaniya da Najeriya, musamman bayan ziyarar ƙasa ta Shugaba Tinubu a Birtaniya da kuma ƙara samun haɓakar kasuwanci da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.