The news is by your side.

Ƴan’uwan Wata Budurwa Sun Zargi Hukumar Hisbah Ta Kano Da Musuluntar Da Ƴarsu Da Ta Ɓace

37

Ƴan’uwan wata budurwa mai shekara 17 daga ƙaramar hukumar Pankshin ta Jihar Filato sun zargi Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da musuluntar da ƴarsu bayan ta ɓace a Jihar Kaduna.

A cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Mayu, 2026, da aka aikewa Kwamishinan Ƴan Sandan jihar Kaduna kuma TheCable ta samu, iyalan sun yi zargin cewa an musuluntar da yarinyar sannan aka aurar da ita.

Rahoton TheCable ya nuna cewa Jinkai Simon, ɗaliba a makarantar St. Bartholomew’s Secondary School da ke Wusasa a Zariya, ta ɓace ne ranar 9 ga Maris bayan ta fita zuwa makaranta.

Kafin faruwar lamarin, tana zaune ne tare da ƴar uwarta Jennifer Simon a unguwar Kuregu da ke Zariya.

Takardar koken da lauyan iyalan ya gabatar ta ce an ga Jinkai a karo na ƙarshe tare da wata maƙwabciyarta mai suna Ruqaiya.

Iyalan sun yi zargin cewa daga baya Ruqaiya ta sanar da su cewa Jinkai ta musulunta sannan an kai ta Jihar Kano inda aka miƙa ta ga Hukumar Hisbah.

Takardar ta kuma zargi hukumar da sauya sunan yarinyar daga Jinkai Simon zuwa Aisha Sani kafin daga bisani a aurar da ita ga wani mutum mai suna Abdulsamad.

Takardar koken ta ce, “Bayan Hisbah ta karɓi yarinyar, ta sauya mata suna daga Jinkai Simon zuwa Aisha Sani sannan ta aurar da ita ga wani Abdulsamad, kuma yanzu ana kiranta Aisha Abdulsamad.”

Sun kuma yi zargin cewa an yi maguɗi wajen sauya shekarunta daga 17 zuwa 19.

Takardun da aka haɗa da koken sun nuna cewa an kai yarinyar gaban wata babbar kotun Jihar Kano inda ta rattaba hannu kan wata takardar shaidar cewa tana da shekara 19 a duniya.

Mahaifan yarinyar sun kuma zargi Hukumar Hisbah da ƙirƙirar takardun amincewa da aka ce su ne suka sanya hannu a kansu domin kammala shirin.

“A ƙoƙarin aiwatar da waɗannan ayyuka ba bisa ƙa’ida ba, Hukumar Hisbah ta kai ga ƙirƙirar takardun amincewa da aka ce iyayen yarinyar ne suka sanya hannu, tare da sa ta rantse a kotu cewa tana da shekara 19,” in ji ƴan’uwan nata.

Sun buƙaci Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Kaduna da ya gudanar da bincike tare da tabbatar da dawo da yarinyar gida cikin ƙoshin lafiya.

An kuma aika kwafen koken zuwa ga Sufeto Janar na Ƴan Sanda, shugaban ƙungiyar CAN ta Jihar Kaduna, Bishop na Anglican Diocese na Wusasa da ke Zariya, ƙungiyar Christian Solidarity Worldwide Nigeria (CSW-N), da kuma ƙungiyar matasan CAN ta Jihar Kaduna.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan zarge-zargen ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.