The news is by your side.

“Babu Wani Ɗan Takara Da Zai Iya Kayar Da Tinubu Daga Yankin Kudu,” – Sansanin Atiku Ya Gargaɗi Ƴan Adawa

44

Sansanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya gargaɗi jam’iyyun adawa da su guji ware tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 ga yankin Kudu kaɗai, yana mai cewa hakan na iya bai wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu damar samun nasara cikin sauƙi.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Atiku kan yaɗa labarai, Olusola Sanni, ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya ce duk da cewa jam’iyyar APC mai mulki na iya ci gaba da tsayar da ɗan takara daga Kudu ƙarƙashin shugaba Tinubu, bai dace ƴan adawa su ɗauki irin wannan mataki ba tare da la’akari da haƙiƙanin lissafin siyasa ba.

Sanarwar ta ce siyasa na buƙatar dabaru, haɗin gwiwa da kuma lissafin cin zaɓe maimakon tafiya da son zuciya ko hujjojin da aka gina kan ra’ayi kaɗai.

“Tambaya ta farko ita ce, ta yaya ɗan takarar adawa daga Kudu zai iya kayar da shugaban ƙasa mai ci daga wannan yanki?” in ji Sanni.

“Tarihin siyasar Najeriya bai taɓa nuna shugaban ƙasa mai ci ya sha kaye a hannun ɗan takarar adawa daga yankinsa ba. Duk wanda ya dage kan hakan kamar ya shiga takara ne domin shan kaye.”

Ya kuma ƙalubalanci hujjar adalcin da ake bayarwa wajen neman ci gaba da miƙa mulki ga Kudu, yana mai cewa zuwa shekarar 2027 yankin Kudun zai kasance ya yi mulki fiye da Arewa a jamhuriya ta huɗu.

“Zuwa 2027, yankin Kudu zai kasance ya yi shekara 18 yana mulkin shugaban ƙasa, yayin da Arewa ta yi kusan shekara 10,” in ji shi.

“Idan Kudu ta ci gaba da riƙe mulki na ƙarin shekara huɗu, bambancin zai ƙara faɗaɗa, wanda hakan ke sanya wahala a fahimci inda adalci yake a irin wannan kafa hujja.”

Sansanin Atiku ya kuma zargi wasu ƴan siyasa da nuna son kai a batun karɓa-karɓar muƙamin shugaban kasa, musamman waɗanda suka goyi bayan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a 2011 bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.

Sanarwar ta amince da muradin yankin Kudu maso Gabas na samar da shugaban ƙasa, amma ta yi gargaɗin kada a mayar da buƙatar zuwa wata yarjejeniya ta siyasa kawai.

“Ba gaskiya ba ne waɗanda suka goyi bayan shugabancin Goodluck Jonathan daga Kudu a 2011 duk da tsammanin Arewa ta ci gaba da mulki, su fito yanzu suna iƙirarin kare adalcin karɓa-karɓa,” in ji sanarwar.

“Ƙa’idoji bai kamata su zama masu tsarki ne kawai ba idan sun dace da buƙatun mutum.”

Sanarwar ta ce yankin Kudu maso Gabas na buƙatar sahihiyar hanya mai ɗorewa domin kai wa ga shugabancin ƙasa, ba wai wata dabara ta siyasa da aka tsara domin biyan buƙatar wani mutum kaɗai ba.

Sansanin Atiku ya buƙaci jam’iyyun adawa su mayar da hankali wajen gina haɗakar siyasar ƙasa mai ƙarfi da za ta iya kayar da gwamnati mai ci maimakon bin abin da ya kira labaran son zuciya.

“Kayar da shugaban ƙasa mai ci na buƙatar haƙiƙanin lissafi da dabaru, ba son zuciya ba,” in ji sanarwar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.