YANZU-YANZU: Najeriya Ta Sanya Maki 150 Na UTME A Matsayin Ƙa’idar Shiga Jami’o’i
Gwamnatin Najeriya ta ayyana maki 150 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya domin shekarar karatu ta 2026.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin ɗin nan yayin taron tsara manufofin shiga manyan makarantu na shekarar 2026 da Hukumar JAMB ta shirya a Abuja.
Haka kuma gwamnati ta sanya maki 150 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga kwalejojin koyon aikin jinya a faɗin ƙasar.
Kwamitin ya kuma ayyana maki 100 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga kwalejojin fasaha da kimiyya, yana mai gargaɗin cewa duk makarantar da ta karya ƙa’idar za ta fuskanci hukunci.
A taron an bayyana cewa duk makarantar da ke son gudanar da tantancewa bayan jarrabawa (post UTME) za ta iya yin hakan, amma ba za ta karɓi sama da naira 2,000 daga ɗalibai ba.
Haka kuma an amince da tsarin kaso 60 zuwa 40 ga jami’o’i da kwalejojin ilimi, inda aka ce kaso 60 na ɗaliban da za a ɗauka su kasance daga fannin kimiyya yayin da kaso 40 za su kasance daga fannin fasaha da zamantakewa.
Sai dai jami’o’i na musamman da kwalejojin fasaha za su yi amfani da tsarin kaso 80 zuwa 20.
A taron manufofin shiga makarantu na shekarar 2025 (bara), JAMB ta sanya maki 150 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga jami’o’i, yayin da kwalejojin koyon aikin jinya suka samu maki 140.