Abdul Samad Rabiu Ya Zama Mutum Na Biyu Mafi Arziƙi A Afirka — Rahoton Bloomberg
Abdul Samad Rabiu, wanda shi ne wanda ya kafa kuma shugaban rukunin kamfanin BUA Group, ya zama mutum na biyu mafi arziƙi a Afirka bayan ya zarce hamshaƙin attajirin Afirka ta Kudu Johann Rupert, kamar yadda rahoton Bloomberg Billionaires Index (BBI) ya nuna.
Rahoton da TheCable ta rawaito ya bayyana cewa, arziƙin BUA ya kai dala biliyan 18.6, lamarin da ya sanya shi na 138 a jerin masu arziƙi a duniya, bayan samun ƙarin kusan dala biliyan 8.47 a farkon shekarar 2026.
A cewar rahoton, ƙaruwar arziƙin na da nasaba da tashin darajar hannayen jarinsa a ɓangarorin masana’antu daban-daban da yake da su.
An kuma bayyana cewa a baya-bayan nan an ƙiyasta arziƙinsa ya kai kusan dala biliyan 15.9, abin da ke nuna irin saurin ci gaban da ya samu cikin watannin kaɗan.
Bloomberg Billionaires Index ya nuna cewa Johann Rupert ya koma matsayi na 153 a duniya bayan da arziƙin sa ya ragu zuwa dala biliyan 17.9 sakamakon asarar kusan dala biliyan 1.76 da ya yi a bana.
Bayanan BBI sun nuna cewa BUA ne attajirin Afirka da ya fi samun ƙarin arziƙi a shekarar 2026, musamman daga harkokin siminti, abinci da masana’antu.
Sabon matsayin ya bar BUA a bayan Aliko Dangote ne kawai a jerin attajiran Afirka.
Dangane da bayanan, Dangote ya ci gaba da kasancewa mutum mafi arziƙi a Afirka da arziƙin dala biliyan 34.4, inda yake matsayi na 66 a duniya bayan ya ƙara kusan dala biliyan 4.38 a dukiyarsa cikin shekarar nan.
Rahoton ya kuma nuna cewa zuwa ranar 7 ga watan Mayu, babu wani ɗan Najeriya da ke cikin jerin attajirai 500 mafiya arziƙi a duniya na Bloomberg baya ga Dangote da BUA.
An bayyana cewa Mike Adenuga, wanda ya kafa kamfanin Globacom, mai arziƙin dala biliyan 6.5, da kuma Femi Otedola, shugaban Geregu Power Plc mai arziƙin dala biliyan 1.3, ba su shiga cikin jerin ba.
Rahoton ya tuna cewa Otedola ya sayar da mafi yawan hannun jarinsa a Geregu Power Plc kan naira tiriliyan 1.088 a shekarar 2025, a wata yarjejeniya da haɗakar bankuna ƙarƙashin jagorancin Zenith Bank Plc suka ɗauki nauyin ta.
A watan Maris, mujallar Forbes ta bayyana BUA a matsayin attajirin Afirka da ya fi samun ƙarin arziki bayan dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 6.1 cikin shekara guda.
Forbes ta ce arziƙin BUA ya ƙaru da kusan kashi 120 cikin 100 zuwa dala biliyan 11.2, abin da ya ɗaga shi zuwa matsayi na uku a jerin masu arziƙi a Afirka daga matsayi na shida da yake a baya.