Rikici ya ɓarke tsakanin Akpabio da wasu manyan Najeriya kan batun shugabancin majalissa
Wata sabuwar taƙaddama ta kunno kai a Majalissar Dattawa ta Najeriya bayan majalisar ta yi gyaran dokokinta wanda zai iya sauya tsarin shugabancinta a majalisa ta gaba da za a kafa bayan zaɓen 2027.
A tsakiyar rikicin akwai shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma da kuma sanatansa mai wakiltar Imo ta Yamma Osita Izunaso.
Rahoton TheCable ya ce, a ranar Talata majalisar dattawan ta gyara dokokinta inda ta ƙayyade cewa sai sanatan da ya yi aƙalla shekara takwas a jere a majalisar kafin ya cancanci tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa ko mataimakinsa.
Sabbin dokokin sun kuma tanadi cewa naɗa sanatoci zuwa manyan muƙamai dole ne ya bi tsarin matsayi da gogewa a majalisar.
Dokar ta Order 5 ta kuma bayyana cewa babu wani sanata da zai iya neman wani babban muƙami sai idan ya yi wa’adi biyu a jere kafin lokacin gabatar da sunansa.
Wannan sauyi ya hana sababbin sanatocin da za su shiga majalissar a shekarar 2027 damar neman manyan muƙamai idan ba su kasance cikin majalissu ta tara da ta goma ba.
Majiyoyi sun shaida wa TheCable cewa gyaran dokokin ya fi kasancewa dabarbarun siyasa fiye da tsarin gudanar da majalissa, musamman domin daƙile wasu fitattun ƴan siyasa masu shirin komawa majalisar dattawa.
Rahoton ya ce Uzodimma na son komawa majalisar dattawa a 2027 bayan ƙarewar wa’adinsa na gwamna, kuma jam’iyyar APC a yankin Imo ta Yamma ta riga ta bayyana shi a matsayin zaɓinta na takarar sanata.
Uzodimma ya taɓa wakiltar Imo ta Yamma daga 2011 zuwa 2019 kafin ya zama gwamna a shekarar 2020 bayan hukuncin kotun ƙoli da ya soke nasarar Emeka Ihedioha a zaɓen gwamnan jihar.
Majiyoyi sun ce gwamnan na duba yiwuwar tsayar da wani na kusa da shi a matsayin ɗan takarar kujerar Orlu a 2027 kafin daga bisani ya karɓi kujerar bayan ƙarewar wa’adinsa a watan Janairun 2028.
Sai dai sabbin dokokin majalisar sun kawo cikas ga yiwuwar Uzodimma ya nemi shugabancin majalisar dattawa ko da ya samu damar komawa majalissar.
A lokacin muhawarar dokokin a ranar Talata, Adams Oshiomhole ne kaɗai ya fito fili yana adawa da sauyin, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara a majalisar washegari bayan amincewa da dokokin.