Tinubu Ya Naɗa Manjo Janar Famadewa Mai Ritaya a Matsayin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Cikin Gida
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa mai ritaya a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Gida, domin ƙarfafa tsarin tsaron cikin gida da haɗin gwiwar hukumomin tsaro a Najeriya.
Sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, inda aka ce naɗin ya nuna ƙudirin gwamnatin Tinubu na inganta ayyukan tattara bayanan sirri da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro wajen tunkarar barazanar tsaro a ƙasar.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya sanya wa hannu, kuma Babban Sakataren Ofishin Ayyuka na Gabaɗaya, Dakta Ibrahim Abubakar Kana, ya fitar, ta bayyana Famadewa a matsayin ƙwararren jami’in soja da leƙen asiri mai gogewa sama da shekara 30.
A cewar sanarwar, Famadewa ya taka muhimmiyar rawa tsakanin shekarun 2015 zuwa 2021 lokacin da yake Babban Jami’in Ma’aikata ga Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro a Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa.
An ce ya jagoranci kafa Cibiyar Haɗa Bayanai ta Intelligence Fusion Centre a ONSA, wadda ta haɗa Hukumar Leƙen Asirin Soja ta DIA, Hukumar Leƙen Asiri ta Waje ta NIA, Hukumar DSS, Rundunar Ƴan Sandan Najeriya da kuma Rundunar Sojin Ƙasa domin inganta tattara bayanai da daidaita tsarin mayar da martanin tsaro.
Bayan ritayarsa daga aikin soja, Famadewa ya yi aiki a matsayin Babban Mai Bincike a Cibiyar Nazarin Sojojin Najeriya da ke Abuja, inda ya ci gaba da bayar da gudunmawa kan gyaran tsarin tsaro da hulɗar jami’an tsaro da fararen hula.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa, sabon naɗin zai taimaka wajen cimma burin gwamnatin sa na samar da Najeriya mafi aminci da tsaro ta hanyar haɗa bayanan sirri da inganta tsare-tsaren kariya a cikin gida.