The news is by your side.

YANZU-YANZU: JAMB Ta Soke Sharaɗin Rubuta UTME Ga Masu Yin Karatun NCE

55

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya (JAMB) ta sanar da cewa daga yanzu masu neman shiga karatuttukan Nigeria Certificate in Education (NCE) a kwalejojin ilimi ba za su sake rubuta jarabawar Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) ba.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin taron tsara manufofin shiga manyan makarantu na shekarar 2026 da JAMB ta gudanar a Abuja.

A ƙarƙashin sabon tsarin, ɗaliban da ke neman shiga kwalejojin ilimi za su buƙaci aƙalla darussa huɗu da suka ci a jarabawar O-level domin samun gurbin karatu.

A cewar ministan, an ɗauki matakin ne domin rage nauyin gudanarwa da ke kan hukumar JAMB wajen gudanar da tsarin shiga manyan makarantu a Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.