The news is by your side.

Aliko Dangote Na Shirin Gina Matatar Mai Ta Dala Biliyan 17 a Kenya

42

Attajirin ɗan kasuwar Najeriya, Aliko Dangote, ya bayyana cewa yana shirin gina wata babbar matatar mai mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana a ƙasar Kenya da ke Gabashin Afirka, bayan ce-ce-ku-ce kan shirin da aka taɓa yi na gina irin wannan matata a Tanzaniya.

Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Financial Times, inda ya ce ya fi karkata zuwa birnin Mombasa saboda tashar jirgin ruwanta ta fi girma da zurfi.

Ya kwatanta tashar ruwan Mombasa da tashar Tanga da ke Tanzaniya, wadda aka fara tunanin gina matatar domin tace man da ake haƙowa daga Uganda.

Dangote ya ƙiyasta cewa aikin zai laƙume tsakanin dala biliyan 15 zuwa 17 wajen kammalawa.

Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta nuna rashin jin daɗinta a makon da ya gabata ga shugaban Kenya William Ruto, tana mai cewa ba a tuntuɓe ta ba game da shirin gina matatar a gaɓar tekun ƙasarta, wanda aka sanar da shi a wani taron bunƙasa ababen more rayuwa da aka gudanar a watan da ya gabata.

Dangote ya ce tattalin arziƙin Kenya ya fi girma kuma yawan amfani da mai a ƙasar ya fi yawa.

Ya kuma bayyana cewa ana iya jigilar ɗanyen mai ta jirgin ruwa ba tare da an jingina matatar da bututun mai da zai ɗauko mai daga filayen mai na Uganda zuwa Tanga da ke Tanzaniya ba.

“A hannun Shugaba William Ruto komai yake. Duk abin da Shugaba Ruto ya ce shi zan yi,” in ji Dangote.

Attajirin ya ce domin aikin ya samu nasara, yana buƙatar gwamnatin Kenya ta samar da fili, tallafin kuɗi daga Gabashin Afirka da kuma kariya daga shigo da mai mai rahusa daga ƙasashe irin su Rasha da Indiya.

“Babu wata matatar mai a duniya da za ta iya rayuwa ba tare da irin wannan kariya ba,” in ji shi.

Dangote ya ce idan an cimma yarjejeniya da gwamnatin Kenya, za a iya fara aikin a wannan shekarar, amma ya ƙara da cewa har yanzu akwai yiwuwar gina matatar a Tanzaniya idan aka warware matsalolin da ke akwai.

Rahoton Financial Times ya bayyana cewa matatar Dangote da ke Legas, wadda aka gina cikin fiye da shekaru goma, ta samu cikakken ƙarfin aiki a daidai lokacin da wasu ƙasashe ke fama da ƙarancin fetur, dizal da man jiragen sama sakamakon matsalolin safarar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz.

Matatar, wadda ake kallon ta a matsayin mafi girman matatar mai mai layi guda a duniya, na tace ganga 650,000 a rana.

Rahoton ya ce saɓanin wasu ƙasashen Afirka irin su Mauritius, Habasha da Zimbabwe da suka fara ƙayyade shan man fetur, Najeriya ba ta fuskanci dogayen layukan neman mai ba har yanzu.

Matatar Dangote ta kuma fara fitar da man jiragen sama zuwa kamfanonin jiragen saman Turai da ke neman ƙarin man domin ci gaba da zirga-zirga.

Har ila yau, rahoton ya ce Dangote ya bai wa Ethiopian Airlines fifiko wajen sayar da man jiragen sama saboda muhimmancin kamfanin a nahiyar Afirka.

Baya ga harkar mai, matatar Dangote na fitar da takin zamani na urea zuwa sassa daban-daban na Afirka, yayin da Najeriya ke amfani da kaɗan daga cikin tan miliyan uku da take samarwa a shekara.

Wani babban jami’i a kamfanin Dangote, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin Iran da rufe mashigin Hormuz ya zama wata babbar dama ta kasuwanci ga kamfanin saboda tashin farashin taki da kuma ƙaruwa a ribar man jiragen sama.

Dangote ya shaida wa Financial Times cewa ribar kamfanonin mai a duniya ta ninka, yana mai cewa ba sa ran kamfaninsa zai yi ƙasa da haka.

Shugaban Kenya William Ruto ya yabawa Dangote, yana mai cewa attajirin ya nuna cewa ƴan Afirka za su iya gina manyan ayyukan raya ƙasa da kansu.

Dangote ya kuma bayyana cewa yana ci gaba da shirin faɗaɗa matatar Legas domin ƙara ƙarfin tace mai zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin watanni 30 masu zuwa.

Ya ce idan hakan ta tabbata, matatar za ta kai kusan kashi 10 cikin 100 na ƙarfin tace mai na Amurka, tare da yin gogayya da kamfanin Reliance Industries na Mukesh Ambani a Indiya.

“Za mu zama masu tasiri wajen ƙayyade farashin kasuwa,” in ji Dangote, yana mai jaddada cewa ya zama wajibi ƴan Afirka su zuba jari a nahiyarsu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.