Malami Ya Yanki Fom ɗin Takarar Gwamnan Kebbi a Inuwar ADC, Ya Yi Wa Ƴan Jihar Manyan Alƙawura
Tsohon Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya yanki fom ɗin tsayawa takarar gwamnan Jihar Kebbi a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin zaɓen shekarar 2027.
Malami ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Asabar, inda ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne saboda ba zai iya ci gaba da yin shiru kan matsalolin da ya ce suna ƙara ta’azzara a jihar ba.
Ya zargi gwamnatin jihar da gazawa wajen magance matsalolin tsaro, talauci, taɓarɓarewar harkokin ilimi da lafiya, da kuma matsin tattalin arziƙi da ke addabar al’umma.
A cewarsa, Jihar Kebbi na fuskantar ɗaya daga cikin manyan matsalolin jin ƙai da shugabanci a Najeriya, yana mai cewa alƙaluman yaran da ba sa zuwa makaranta, talauci mai ɗimbin yawa, mace-macen mata masu juna biyu, rashin abinci mai gina jiki da matsalolin tsaro sun kai matakin matuƙar damuwa.
Malami ya ce fiye da kashi 67 cikin 100 na yara masu shekaru tsakanin shida zuwa 15 ba sa zuwa makaranta, yayin da sama da kashi 88 cikin 100 na yaran jihar ke rayuwa cikin matsanancin talauci ta fannoni daban-daban.
Tsohon ministan ya kuma nuna damuwa kan yanayin harkokin lafiya a jihar, inda ya ce mace-macen mata masu juna biyu na ci gaba da ƙaruwa, yayin da al’ummomin karkara da dama ba su da isassun cibiyoyin kula da mata masu juna biyu da sauran muhimman ayyukan lafiya.
Game da matsalar tsaro kuwa, Malami ya ce al’ummomi da dama a faɗin jihar na ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane, lamarin da ya tilasta wa manoma barin gonakinsu tare da jefa harkokin kasuwanci cikin fargaba.
Ya zargi gwamnatin da ke mulki da karkatar da hankali daga muhimman abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a a daidai lokacin da al’umma ke fama da matsin tattalin arziƙi da rashin tsaro.
Malami ya ayyana abin da ya kira “dokar ta-baci kan rashin kyakkyawan shugabanci” a jihar, yana mai alƙawarin mayar da hankali kan dawo da tsaro, inganta ilimi, ƙarfafa harkokin lafiya, farfaɗo da noma da samar wa matasa dama idan aka zaɓe shi gwamna a shekarar 2027.
Ya ce burinsa ya samo asali ne daga son yin hidima wa al’umma, riƙon amana da samar da ci gaba mai ɗorewa, yana mai cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen abin da ya bayyana a matsayin shugabanci marar tasiri da farfaganda.
Malami ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi da su mara masa baya domin sake gina jihar ta zama wuri mafi aminci da ci gaba.
“Ba za a ja da baya ko miƙa wuya ba a wannan fafutukar ta ceto jiharmu,” in ji shi.