Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta sanar da cewa za ta gudanar da taron tsara manufofin shiga manyan makarantu na shekarar 2026 ranar Litinin, inda za a tattauna muhimman batutuwan da suka shafi tsarin ɗaukar ɗalibai a manyan makarantu a Najeriya, ciki har da amincewa da mafi ƙarancin makin shiga makarantu.
A cikin wata sanarwa da mai ba hukumar shawara kan hulɗa da jama’a, Fabian Benjamin, ya fitar ranar Lahadi, JAMB ta ce Ministan Ilimi ne zai jagoranci taron, wanda zai haɗa masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi domin tsara “ƙa’idojin gudanar da shiga manyan makarantu na shekarar 2026 a Najeriya.”
Sanarwar ta bayyana cewa zaman zai kuma duba tare da amincewa da ma’aunin shiga makarantu, ciki har da “ƙayyade mafi ƙarancin makin da za a iya amincewa da shi wajen bayar da guraben karatu,” wanda aka saba amfani da shi wajen shiga jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi.
Hukumar ta kuma bayyana cewa taron na bana zai samu halartar tawaga daga ƙasar Saliyo, ciki har da Mataimakin Ministan Ilimi na ƙasar, Sarjoh Aziz Kamara, da shugabannin jami’o’i biyu — Farfesa Edwin Momoh na Jami’ar Ernest Bai Koroma University of Science and Technology da Farfesa Bashiru Koroma na Jami’ar Njala.
A cewar sanarwar, jami’an Saliyo sun zo Najeriya ne domin nazarin tsarin bai ɗaya na shiga manyan makarantu da Najeriya ke amfani da shi, yayin da ƙasarsu ke tunanin kafa irin wannan hukuma domin daidaita tsarin shiga makarantu.
Tun da farko, an yi wa tawagar bayani kan yadda JAMB ke gudanar da jarabawa da tsarin bayar da guraben karatu a hedikwatar hukumar da ke Bwari.
A yayin taron manufofin, ana sa ran tawagar za ta lura da yadda masu ruwa da tsaki ke shiga cikin tsarin bayar da guraben karatu a Najeriya, wanda JAMB ta bayyana a matsayin tsarin haɗin gwiwa mai ɗauke da sassa daban-daban.
Rahotanni sun ce tawagar ta nuna godiya ga hukumar JAMB, tana mai cewa yawaitar masu neman shiga manyan makarantu a Saliyo ya haifar da ƙalubale mai yawa, yayin da tsarin Najeriya ke bayar da mafita ga matsalolin da suka daɗe suna neman warakarsu.
Hukumar ta sake jaddada muhimmancin rawar da take takawa a tsarin ilimin ƙasar, tana mai cewa tsarin bayar da guraben karatu da take jagoranta na da matuƙar tasiri wajen tsara shiga manyan makarantu a Najeriya.