Tana Neman ta Leƙo ta Komawa Vijay Mai Adda, Bayan Jam’iyyarsa ta Gaza Samun Rinjayen Kujeru a Tamil Nadu
Jihar Tamil Nadu ta India na fuskantar zafafan tattaunawar siyasa bayan jam’iyyar Tamilaga Vettri Kazhagam (TVK) ƙarƙashin jagorancin C Joseph Vijay (Mai Adda) ta zama jam’iyya mafi yawan kujeru a zaɓen majalisar dokokin jihar na shekarar 2026 amma ta kasa samun rinjayen da ake buƙata domin kafa gwamnati.
Rahoton The Times of India ya ce, TVK ta samu kujeru 108 cikin kujeru 234 na majalisar dokokin jihar, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar Dravida Munnetra Kazhagam bayan ta yi wa’adi guda kacal.
Sai dai domin kafa gwamnati, ana buƙatar kujeru 118, kuma ana sa ran Vijay zai bar ɗaya daga cikin kujerun biyu da ya lashe, abin da zai iya rage yawan kujerun jam’iyyarsa.
Jam’iyyar Indian National Congress ta bayyana goyon bayanta ga Vijay bayan wasu manyan shugabanninta sun gana da shi a hedikwatar jam’iyyar da ke Chennai.
Matakin ya fusata jam’iyyar DMK wadda ta zargi Congress da watsi da tsohon ƙawance da kuma raunana haɗin kan ƴan adawa kafin zaɓukan ƙasa masu zuwa.
A gefe guda kuma, jam’iyyar All India Anna Dravida Munnetra Kazhagam karkashin jagorancin Edappadi K Palaniswami ta fara nazarin yiwuwar bai wa TVK goyon baya ba tare da sanya wani sharaɗi ba domin kafa gwamnati mai ƙarfi.
Sai dai majiyoyi sun shaida wa The Times of India cewa, tattaunawar tsakanin ɓangarorin biyu ta rushe bayan shugabannin AIADMK sun ce ba su samu amsa daga ɓangaren TVK ba na tsawon sa’o’i da dama.
Daga baya jam’iyyar AIADMK ta janye tayin nata tare da bayyana cewa ba za ta shiga wani ƙawance da DMK ba.
Vijay ya kuma gana da gwamnan jihar Tamil Nadu, R N Ravi Arlekar, domin gabatar da buƙatarsa ta kafa gwamnati yana mai cewa yana da isassun ƙuri’un ƴan majalisa.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce gwamnan ya buƙaci a gabatar masa da rubutattun takardun goyon baya daga isassun ƴan majalisa kafin a ci gaba da shirye-shiryen rantsar da sabuwar gwamnatin.
Ƙananan jam’iyyu irin su Viduthalai Chiruthaigal Katchi da jam’iyyu masu sauƙin ra’ayin jari-hujja na CPI da CPM har yanzu ba su yanke hukunci kan ko za su mara wa TVK baya ba, yayin da Indian Union Muslim League da wasu jam’iyyun suka ci gaba da goyon bayan DMK.
Firaministan jihar mai barin gado, MK Stalin, ya ce jam’iyyarsa ta DMK za ta zauna a matsayin ƴar adawa tare da “sauraro ba tare da yin katsalandan ba na tsawon watanni shida”, yayin da ya kuma nuna shakku kan ko TVK za ta iya cika manyan alƙawuran yakin neman zaɓenta.