The news is by your side.

Daga Yanzu Dole Ne a Yi Wa Kowanne Ɗalibin Sakandare Gwajin Ƙwaya Duk Shekara a Najeriya – Gwamnati

42

Gwamnatin tarayya ta umurci a riƙa yi wa sabbin ɗalibai da waɗanda ke ci gaba da karatu a makarantun sakandare a faɗin Najeriya gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi.

Sabuwar dokar na ƙunshe cikin “National Implementation Guidelines Against Drug and Substance Use in Schools in Nigeria” da aka tanada domin makarantun sakandare.

Gwamnatin ta ce manufar tsarin ita ce samar da yanayin koyarwa da koyo mai kyau ta hanyar rage illar da amfani da miyagun ƙwayoyi ke yi ga lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma karatun ɗalibai.

Matakin na zuwa ne yayin da ake nuna damuwa kan ƙaruwar amfani da miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa a Najeriya.

A ƙarƙashin sabon tsarin, duk sabon ɗalibin da zai shiga makarantar sakandare dole ne a yi masa gwajin ƙwayoyi kafin a ba shi gurbin karatu.

“Dukkan sabbin ɗalibai za a yi musu gwajin miyagun ƙwayoyi da sauran matakan da makarantu suka amince da su kafin fara karatu,” in ji takardar, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Takardar ta kuma ce ana sa ran makarantu za su riƙa gudanar da irin wannan gwaji ga ɗaliban da suka dawo makaranta aƙalla sau ɗaya a kowace shekara ta karatu.

“An haramta wa ɗalibai amfani ko mallakar miyagun ƙwayoyi ko wasu abubuwan maye ba tare da izinin hukumomin makaranta ba,” in ji dokar.

Tsarin ya kuma tanadi matakai uku na gwaji da bayar da kulawa ga ɗaliban da aka samu suna amfani da miyagun ƙwayoyin.

A cewar dokar, manufar ita ce gano ɗaliban da ke buƙatar taimako tare da tabbatar da ingantaccen yanayi mai lafiya a makarantu.

“Ɗaliban da aka samu suna amfani da miyagun ƙwayoyi za su fara samun shawarwari da kulawa kamar yadda hukumomin makaranta suka ga ya dace,” in ji tsarin.

“Idan aka sake samun ɗalibi da laifi a karo na biyu, makaranta za ta tura shi wajen ƙwararru domin samun kulawa ta musamman.”

Dokar ta ce idan aka sake samun ɗalibi da irin wannan laifi a karo na uku, za a dakatar da shi daga makaranta na wani lokaci domin samun magani da gyaran hali daga ƙwararru.

Tsarin ya kuma tanadi bayar da shawarwari kafin da bayan gudanar da gwajin.

“Shawarwarin kafin gwaji na taimaka wa mutum ya fahimci abin da za a yi, rage tsoro da ƙarfafa samun haɗin kai,” in ji dokar.

“Shawarwarin bayan gwaji kuma na taimaka wa mutum ya karɓi sakamakon tare da samun taimakon da ya dace.”

Gwamnatin ta kuma umarci kowace makaranta da ta kafa kwamitin ladabtarwa domin tabbatar da bin dokar, tare da gargaɗin cewa duk wani tashin hankali da ya shafi amfani da miyagun ƙwayoyi ya kamata a kai rahotonsa ga hukumomin tsaro.

Haka kuma, tsarin ya ce ɗaliban da suka ƙi bin matakan kulawa ko gyaran hali za a dakatar da su daga zuwa makaranta har sai an tabbatar da lafiyarsu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.