The news is by your side.

Dr. Magaji Dau Aliyu Ya Samar Wa Matasa 40 Aikin Yi a Jigawa

177

Daraktan Janar kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Sheda Science and Technology Complex, Dr. Magaji Dau Aliyu, ya samar da aikin wucin-gadi ga kusan matasa 40 a Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa ta hanyar wani shirin ƙididdigar gidajen masu amfani da wutar lantarki.

Ana gudanar da shirin ne haɗin gwiwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), domin tattara sahihan bayanai kan masu amfani da wutar lantarki a gidaje da nufin inganta tsarin rarraba wuta mai ɗorewa a yankin.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Darakta Janar kan harkokin yaɗa labarai, Hassan Nakudu, ya fitar.

Nakudu ya bayyana cewa matasan da aka ɗauka aikin za su gudanar da ƙididdigar gidaje daga gida zuwa gida, tattara bayanai da kuma rubuta bayanan masu amfani da wutar lantarki a faɗin ƙaramar hukumar.

Sanarwar ta ce waɗanda suka amfana da shirin, waɗanda aka zaɓo daga Birnin Kudu da maƙwabtan al’ummomi, sun riga sun fara samun horo mai zurfi a ɗakin taro na Dau Aliyu Hall da ke Birnin Kudu domin ƙarfafa musu ƙwarewar fasaha da gudanarwar da ake buƙata.

A cewar Nakudu, bayan kammala horon, za a tura masu aikin zuwa gundumomi da al’ummomi daban-daban a faɗin ƙaramar hukumar domin gudanar da aikin da zai taimaka wajen ƙarfafa bayanan kwastomomin KEDCO da kuma inganta samar da wutar lantarki.

Ya ce shirin ba wai kawai zai taimaka wajen inganta samar da wuta ba ne, har ma zai samar wa matasa damar samun kuɗaɗen shiga, rage rashin aikin yi da kuma daƙile shiga ayyukan ta’addanci da miyagun halaye.

“Shirin na daga cikin ƙoƙarin Dr. Magaji Dau Aliyu na ci gaba da ƙarfafa matasa ta hanyar samar musu da ayyuka masu amfani da za su inganta rayuwarsu tare da taimakawa ci gaban al’umma,” in ji sanarwar.

Mataimakin ya kuma yaba wa tsohon ɗan Majalisar Wakilai kuma tsohon shugaban Kwamitin Majalisar kan Wuta da Makamashi bisa ci gaba da nuna jajircewa wajen tallafa wa matasa, bunƙasa ababen more rayuwa da kuma shirye-shiryen da ke inganta rayuwar jama’a a matakin ƙasa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.