The news is by your side.

Atiku, Amaechi da Hayatu-Deen Sun Yanki Fom ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a Inuwar ADC

21

Gasar neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin zaɓen 2027 na ci gaba da ɗaukar zafi bayan Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen sun yanki fom ɗin takara tsakanin ranar Juma’a da Asabar, kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya rawaito.

Mohammed Hayatu-Deen ne ya fara karɓar fom ɗin, lamarin da ya sa ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na farko da ya bayyana a jam’iyyar ADC domin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ADC ta bayyana Hayatu-Deen a matsayin masani kan tattalin arziƙi, ɗan kasuwa, mai zuba jari da kuma jagoran kamfanoni ɗan asalin Jihar Borno, tana mai cewa yana da gogewa mai faɗi a fannin gudanar da tattalin arziƙi da bunƙasa ƙasa.

Rahoton ya ce magoya baya da mambobin jam’iyyar sun tarɓe shi da farin ciki lokacin da ya yanki fom ɗin.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, shi ma ya shiga takarar, kuma ana sa ran zai mayar da fom ɗinsa ranar Litinin a sakatariyar ADC da ke Abuja.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na X, ta ce Atiku Abubakar ya karɓi takardar shaidar biyan kuɗin neman takara domin fafatawa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Jam’iyyar ta ce matakin na nuna wani gagarumin ci gaba a yunƙurin samar da sabon tsarin shugabanci, haɗa kan jama’a da kuma samar da jagorancin da jama’a ke da tasiri a cikinsa.

Shi ma Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon minista a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yanki fom ɗin takarar shugaban ƙasa na ADC.

Wani jigo a jam’iyyar adawar, John Oyegun, ne ya karɓi fom ɗin a madadinsa tare da rakiyar tsohon Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi; Sanata Nura Abatemi; da Ike Bishop Okoronkwo, shugaban kamfanin Bishop Plus Media Services, da sauran fitattun ƴan siyasa.

Lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da kuma makwanni kafin jam’iyyun siyasa su gudanar da tarukansu na zaɓen fidda gwanaye.

Jam’iyyar ADC ce babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, sai dai a baya-bayan nan ta rasa wasu tsoffin ƴan takarar shugaban ƙasa guda biyu, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, waɗanda suka fice daga jam’iyyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.