Gwamnatin Pakistan ta musanta rahotannin da ke zarginta da bai wa jiragen yaƙin Iran mafaka domin kare su daga yiwuwar harin Amurka yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Tehran da Washington ke fuskantar barazana.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana hakan ranar Talata bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar na “kan na’urar taimakawa numfashi”.
Trump ya yi wannan furuci ne bayan rahoton CBS News da ya ce Iran ta kai wasu jiragen soja ciki har da jirgin leƙen asiri samfurin RC-130 zuwa sansanin sojin saman Pakistan na Nur Khan da ke kusa da Rawalpindi bayan tsagaita wutar ranar 8 ga Afrilu.
A cikin sanarwar da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana rahoton a matsayin “mai ruɗani kuma mai neman jan hankali”, tana mai cewa jiragen sun isa ne domin ayyukan diflomasiyya da suka shafi tattaunawar jami’an Amurka da Iran a Islamabad ranar 11 ga Afrilu.
Ma’aikatar ta ce jiragen Iran da na Amurka duk sun yi amfani da sansanin, kuma babu wata alaƙa tsakanin jiragen Iran da shirye-shiryen soja.
Rahoton CNN ya ce wasu jami’an gwamnatin Trump na zargin Pakistan da gabatar wa Amurka wani salo mai sauƙi game da matsayin Iran fiye da yadda lamarin yake a zahiri.
Wani jami’in Pakistan da ya zanta da Al Jazeera ya ce Islamabad na ƙoƙarin kasancewa mai shiga tsakani cikin adalci domin warware rikicin.
Sanatan Amurka Lindsey Graham ya yi kira da a sake nazarin rawar da Pakistan ke takawa wajen shiga tsakani idan rahoton CBS ya tabbata gaskiya.
Sai dai masani kan harkokin tsaro a Jami’ar Lahore, Syed Ali Zia Jaffery, ya shaida wa Al Jazeera cewa, Pakistan ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsagaita wuta duk da rashin yarda tsakanin ɓangarorin.
A halin yanzu, Amurka na son Iran ta yi watsi da shirinta na nukiliya, yayin da Tehran ta dage cewa ba za a fara tattaunawar nukiliya ba sai an ɗage takunkumi da killace tashoshin jiragen ruwanta.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce idan tattaunawa ta gaza warware rikicin, Isra’ila da Amurka na iya komawa matakin soja.