Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano kuma tsohon Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya gana da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, a Abuja ranar Talata domin tattauna harkokin siyasa kafin zaɓen 2027.
Rahoton PUNCH ya ce tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi, Abba Abubakar Kabir Bichi, sun halarci taron da aka gudanar a sirri.
A wata sanarwa da Gwarzo ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan harkokin siyasa a Kano ta Arewa da kuma al’amuran jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi musu fatan alheri da nasara a tafiyarsu ta siyasa.
Taron na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an tantance Gwarzo a matsayin mai neman takarar kujerar Sanatan Kano ta Arewa ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress.
Rahotanni sun nuna cewa Kano ta Arewa na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan yankunan siyasa a Jihar Kano gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Daga cikin fitattun ƴan siyasar yankin akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda ke riƙe da kujerar Sanatan Kano ta Arewa a halin yanzu.
Sauran manyan jiga-jigan siyasar yankin sun haɗa da sabon Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, da kuma Abba Kabir Bichi da T-Gwarzo.
Rahoton ya ƙara da cewa wani mai neman takarar kujerar Sanatan Kano ta Arewa, Mahmoud Baba Bichi, ya janye daga takarar bayan rahotannin shiga tsakani da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi domin tabbatar da haɗin kan jam’iyyar.