Sheikh Sani Abdulkadir, mutum na shida cikin waɗanda ake tuhuma a shari’ar yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana cewa tun farko ya gargaɗi waɗanda ake zargin cewa shirinsu ba zai yi nasara ba.
Rahoton Zagazola Makama, wata kafar yaɗa labarai da ke mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya ce, Sheikh Sani ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ci gaba da sauraron ƙarar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
An kunna wani bidiyo a kotun inda Sheikh Sani, wanda malamin addinin Musulunci ne, ya amince cewa ya karɓi kuɗi domin yin addu’o’in samun nasarar shirin, amma ya ce ya gargaɗi waɗanda ake zargin cewa wasu daga cikinsu za su tona musu asiri.
A cikin bidiyon, Sheikh Sani ya ce, ya san mutumin da ake zargin jagorantar shirin mai suna Maaji ƙasa da shekara guda, kuma wani mutum mai suna Sanda ne ya tuntuɓe shi domin neman taimakon addu’a.
Ya ce Sanda ya gaya masa cewa “Ogansa” na shirin yin juyin mulki kuma yana son sanin ko shirin zai yi nasara.
Sheikh Sani ya ce bayan ya yi addu’o’in, ya sanar da su cewa shirin zai lalace saboda wasu mutane biyu za su tona asirin waɗanda ke ciki.
Ya ce daga baya waɗanda ake zargin sun sake neman ya yi ƙarin addu’a domin hana mutanen biyu yin magana.
Rahoton Zagazola ya ce daga bisani an aika wa malamin kuɗaɗe domin addu’a da bayar da sadaka, tare da tura sunayen mutanen da ake zargin suna cikin shirin domin saka su a addu’a.
Sheikh Sani ya ce, ya fara jin labarin kama waɗanda ake zargin ne ta kafafen yaɗa labarai bayan Sanda ya sanar da shi cewa ba a samu Maaji ba har tsawon kwanaki huɗu.
Ya jaddada cewa kuɗaɗen da ya karɓa na addu’a ne kawai, ba don tallafa wa yunƙurin juyin mulki ba.
Malamin ya kuma amince cewa ya san juyin mulki na nufin sojoji su kifar da gwamnati, amma ya ce bai kai rahoton shirin ga hukumomi ba saboda bai san wanda zai sanar ba.
A cewarsa, an kama shi ne bayan ya je Hukumar EFCC domin warware matsalar da aka samu kan asusun bankinsa.
Ya ce an gayyace shi ofishin hukumar domin bayyana tushen kuɗaɗen da suka shiga asusun nasa.
Sheikh Sani ya musanta cewa ya yi wani furuci mai nasaba da juyin mulki yayin da yake hannun EFCC, yana mai cewa ba a yi masa duka ko wata azabtarwa ba a hukumar, kuma duk bayanan da ya bayar ganin damarsa ne ba tilasta shi aka yi ba.
Bayan nuna bidiyon, masu gabatar da ƙara sun nemi kotu ta amince da bayanan da dukkan waɗanda ake tuhuma shida suka bayar ga kwamitin bincike na musamman da jami’an soja.
Sai dai lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun yi adawa da hakan, suna masu cewa an samu bayanan ne ta hanyar tilastawa ko kuma an karya dokar Administration of Criminal Justice Act (ACJA).
Lauyoyin sun bayyana cewa ba a sanar da waɗanda ake tuhuma haƙƙinsu na samun lauya ba, sannan akwai saɓani tsakanin bidiyon da rubutattun bayanai, tare da zargin amfani da tilastawa da azabtarwa.
Lauyan wanda ake tuhuma na biyar ya kuma buƙaci kotu ta gudanar da bincike daban-daban kan bayanan kowane wanda ake tuhuma maimakon haɗa su gaba ɗaya.
Sai dai masu gabatar da ƙara sun buƙaci kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen, suna masu cewa doka ba ta wajabta gudanar da shari’a daban ga kowane mutum ba.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin cewa za a gudanar da shari’ar tantance sahihancin bayanan gaba ɗaya a lokaci guda.
Daga nan kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga Mayu, 2026.
A ranar 22 ga Afrilu ne, gwamnatin tarayya ta gurfanar da mutane shida kan zargin shirya juyin mulki domin hamɓarar da gwamnatin Shugaba Tinubu.
An gurfanar da su ne a ƙarƙashin tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi ta’addanci, inda dukkansu suka musanta laifukan.
Wadanda ake tuhuma a ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CR/206/2026 sun haɗa da Mohammed Gana, Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya daga rundunar ruwa, Ahmed Ibrahim jami’in ɗan sanda, Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da kuma Sheikh Sani Abdulkadir.
An kuma ambaci tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, a cikin ƙarar, inda aka ce har yanzu yana gudun hijira.
Ana zargin waɗanda ake tuhuma da ƙoƙarin tayar da yaƙi a Najeriya tare da aikata laifukan cin amanar ƙasa da ta’addanci.