Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana goyon bayansa ga ci gaba da miƙa shugabancin ƙasa zuwa Kudancin Najeriya a zaɓen 2027, tare da nuna shirinsa na zama mataimakin Peter Obi idan haɗakar jam’iyyun adawa ta amince da hakan.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin PrimeTime na gidan talabijin na Arise TV.
Ya ce shugabannin haɗakar siyasar sun cimma matsaya kan goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu domin tabbatar da daidaito da kuma rage cece-kuce kan karɓa-karɓar mulki tsakanin yankunan Najeriya.
A cewarsa, hakan ya sanya Peter Obi zama wanda ake ganin zai fi ƙarfi wajen samun tikitin takarar shugaban ƙasa na haɗakar kafin zaɓen 2027.
“Wannan shi ne abin da ya dace,” in ji Kwankwaso lokacin da aka tambaye shi ko Obi ne zai zama babban ɗan takarar haɗakar.
Ya ƙara da cewa, “Idan jam’iyya ta yanke shawarar cewa ni zan zama mataimakin duk wani ɗan takara daga Kudu a irin wannan yanayi, zan yi farin cikin haɗa kai da shi.”
Kwankwaso ya ce an ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki, waɗanda a cewarsa suka fahimci cewa Najeriya na buƙatar shugabanci mai inganci da jajircewa fiye da ci gaba da muhawara kan yankin da shugaban ƙasa zai fito.
“Abin da ya fi muhimmanci yanzu ba shugaban ƙasa daga Arewa ko Kudu ba ne,” in ji shi.
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne samun shugabanci mai nagarta, mutanen da suke da ƙwazo da jajircewa wajen bai wa ƙasa shugabancin da ta dace da shi.”
Tsohon ministan tsaron ya ce ƴan Najeriya da dama, musamman matasa, sun fi mayar da hankali kan shugabannin da za su magance matsalolin tsaro, wahalar tattalin arziƙi da rashin ingantattun ababen more rayuwa maimakon batun ƙabila ko addini.
Ya kuma yabawa Peter Obi, yana mai bayyana shi a matsayin amintaccen abokin tafiya wajen sauya alƙiblar Najeriya.
“Ni kaina, ban taɓa ganin wata haɗaka mafi kyau ba, ko da za a ba ku lokaci mai tsawo ku nemo waɗanda za su fi mu wajen yin abin da ya dace ga ƙasar nan,” in ji Kwankwaso.
Ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa za a iya samun saɓani tsakaninsa da Obi idan suka tsaya takara tare, yana mai cewa gogewarsa a siyasa ta nuna cewa shugabanni da mataimakansu na iya yin aiki tare cikin nasara.
Kwankwaso ya ce yawan son kai da kwaɗayin mulki ne ke haddasa rikice-rikice a gwamnatoci.
“Akwai ayyuka masu yawa da ya kamata a yi fiye da rikicin neman iko,” in ji shi.
Ya kuma kare haɗin gwiwar da ke ƙara ƙarfi tsakanin tafiyar Kwankwassiya da ƙungiyar magoya bayan Obi da ake kira Obidient Movement, yana mai cewa ɓangarorin biyu sun riga sun fara aiki tare a sassa daban-daban na Najeriya da kuma ƙasashen waje.
A cewarsa, haɗakar na samun ƙaruwar goyon bayan ƴan Najeriya da ba su gamsu da halin da ƙasar ke ciki ba.
Da yake magana kan jam’iyyar APC mai mulki, Kwankwaso ya ce duk da yawan jihohin da jam’iyyar ke iko da su, ƴan Najeriya na ƙara nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da gwamnati a matakin tarayya da jihohi.
“Zaɓen 2027 zai kasance tsakanin ƴan Najeriya da shugabanni,” in ji shi, yana mai cewa mutane da dama na neman sauyi saboda matsalolin tattalin arziƙi, tsaro da gazawar shugabanci.
Ya kuma soki shugabannin siyasa da ke raina tasirin matasa da kafafen sada zumunta wajen sauya yanayin siyasa a ƙasar.
Kwankwaso ya jaddada cewa haɗakar adawa ta mayar da hankali ne wajen gina tafiya mai faɗi da za ta samar da abin da ya kira “ingantacce kuma sahihin shugabanci” ga Najeriya.