Najeriya Ta Ware Naira Biliyan 250 Domin Gina Ɗakunan Kwanan Ɗalibai a Manyan Makarantu

Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe kusan naira biliyan 250 a shekarar 2026 domin gina ɗakunan kwanan ɗalibai a manyan makarantu a faɗin ƙasar.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage matsalar rashin masauƙi a manyan makarantu da kuma inganta walwala da tsaron ɗalibai.

Ministan Ilimi, Dakta Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa shirin zai samar da dubban guraben kwanciya ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

A cewarsa, gwamnati za ta kashe naira biliyan 100 wajen gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu ɗaukar ɗalibai 500 a kusan jami’o’i 50, inda kowace jami’a za ta samu aikin da ya kai na naira biliyan biyu.

Ya ce wani ɓangare na shirin zai tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa guda 24 tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda za su samar da tsakanin guraben kwanciya 1,200 zuwa 1,500 a kowace makaranta.

A ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwar, gwamnatin tarayya za ta bayar da naira biliyan ɗaya ga kowanne aiki, yayin da masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu za su samar da kusan naira biliyan uku.

Ministan ya ce za a aiwatar da shirin ne ta hannun Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na TETFund, tare da faɗaɗa ɗakunan kwanan ɗalibai da ake da su a faɗin ƙasar.

DalibaiIlimiNajeriya
Comments (0)
Add Comment