Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da ci gaba da amfani da shekaru 16 a matsayin mafi ƙarancin shekarun shiga manyan makarantu a ƙasar.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan a ranar Litinin ɗin nan yayin taron tsara manufofin shiga manyan makarantu na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
A cewarsa, matakin ya biyo bayan tattaunawa da nazarin manufofi domin samar da daidaito tsakanin bai wa ɗalibai dama da kuma tabbatar da shirinsu na ilimi.
Alausa ya ce duk da cewa akwai ɗalibai masu baiwa ta musamman, dole ne a kula da irin waɗannan lokuta cikin ƙa’idoji masu tsauri domin kare martabar tsarin ilimi.
Ministan ya kuma jaddada cewa duk wata shiga makaranta da aka yi ba tare da bin tsarin Central Admissions Processing System (CAPS) na JAMB ba haramtacciya ce kuma ba za a amince da ita ba.
Ya yi gargaɗin cewa duk makarantar da aka samu da karya ƙa’idar za ta iya fuskantar hukunci har da dakatar da lasisin aikinta.
Alausa ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da bin ƙa’idojin shiga makarantu domin dawo da amincewa da tsarin ilimin ƙasar.
Ministan ya kuma yi magana kan ƙudirin gwamnati na faɗaɗa amfani da fasahar zamani a harkar ilimi, yana mai cewa amfani da jarabawar kwamfuta da ƙwarewar fasahar dijital ya zama wajibi.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙarfafa matakan yaƙi da satar amsa ta hanyar inganta tsarin tantancewa da sa ido.