Iran Ta Zargi Amurka da Gabatar da Sharuɗɗa Na Rashin Adalci a Tattaunawar Tsagaita Wuta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya zargi Amurka da gabatar da sharuɗɗa “marasa ma’ana” kuma na nuna son kai a tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen yaƙin da ke gudana, yayin da ɓangarorin biyu ke ci gaba da tsagaita wuta cikin yanayi mai cike da rashin tabbas.

Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Iran sun rawaito cewa Tehran ta aika da martani ga wata shawarar Amurka ta kawo ƙarshen yaƙin ta hannun Pakistan ranar Lahadi, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana sharuɗɗan Iran a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba gaba ɗaya.”

Da yake jawabi a wani taron manema labarai ranar Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce shawarar Iran na kawo ƙarshen rikicin da kuma sake buɗe mashigin Hormuz ta kasance halastacciya kuma mai nuna karamci.

Ya buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin da ke gudana a yankin tare da sakin kadarorin Iran da aka daskarar a ƙasashen waje a matsayin martani ga sabon tayin Amurka.

“Ba mu nemi wani rangwame ba. Buƙatarmu halastacciya ce: kawo ƙarshen yaƙi, ɗage takunkumin Amurka da kuma sakin kadarorin Iran da aka daskarar saboda matsin lambar Amurka,” in ji Baghaei.

Ya ƙara da cewa tabbatar da zirga-zirga lafiya ta mashigin Hormuz da samar da tsaro a yankin da Lebanon na daga cikin buƙatun Iran.

Trump ya bayyana a shafinsa na Truth Social cewa zai yi watsi da martanin Tehran, duk da cewa bai bayyana cikakken abin da tayin ya ƙunsa ba.

“Na karanta martanin da wakilan Iran suka bayar. Ban ji daɗinsa ba — gaba ɗaya ba abin amincewa ba ne,” in ji shugaban Amurkan.

Masanin harkokin siyasa na Jami’ar American University of Rome, Andrea Dessi, ya ce alamu na nuna cewa ɓangarorin biyu na ci gaba da tsayawa kan matsayinsu ba tare da sassauci ba.

Ya ce hakan na ƙara jefa tattalin arzikin duniya da al’ummar yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya cikin mawuyacin hali.

Bayan furucin Trump, farashin ɗanyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 4.65 cikin 100 zuwa dala 99.95 kowace ganga a kasuwannin Asiya ranar Litinin ɗin nan.

Farashin man West Texas Intermediate (WTI) na Amurka shi ma ya ƙaru da fiye da kashi huɗu cikin 100 zuwa dala 105.5 kowace ganga saboda fargabar ƙaruwar tangarɗa ga safarar mai ta mashigin Hormuz.

Baghaei ya kuma yi tsokaci kan shirin ƙasashen Turai na tura jiragen ruwa zuwa yankin domin tabbatar da zirga-zirga lafiya ta mashigin Hormuz, wadda Iran ta taƙaita zirga-zirga a cikinsa tun watan Maris.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Birtaniya Keir Starmer na jagorantar ƙawancen ƙasashe sama da 50 da ke shirin taimakawa wajen dawo da harkokin sufuri ta ruwa a yankin bayan yaƙin.

Sai dai Baghaei ya gargaɗi ƙasashen Turai da kada su faɗa cikin abin da ya kira “girman kai” na Amurka da Isra’ila.

Ya ce duk wani tsoma baki a mashigin Hormuz ko Tekun Fasha zai ƙara dagula al’amura tare da haddasa tashin farashin kayayyaki a duniya.

AmurkaHormuzIranTrump
Comments (0)
Add Comment