Matashi Mai Naƙasa Ya Tsallake Tantancewar APC Domin Shiga Takarar Majalisar Tarayya a Kaduna

Mahmud Sadis Buba, wani matashi mai shekara 30 da ke rayuwa da naƙasa, ya tsallake tantancewar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin neman kujerar Majalisar Wakilai daga Jihar Kaduna.

Buba, wanda aka fi sani da Abin Al-Ajabin Zazzau, na neman wakiltar mazaɓar Sabon Gari ta tarayya.

Matashin na rayuwa da matsalar wadanci (dwarfism,) wadda ke shafar girma da ci gaban jiki.

Ya ja hankalin mutane a kafafen sada zumunta bayan wani bidiyo daga zaman tantancewarsa na APC ya bayyana a intanet.

Yayin tantancewar, Buba ya bayyana cewa shi ne na fari cikin ƴaƴa tara kuma yana da shaidar kammala makarantar sakandare.

Da yake bayanin dalilin shiga takara, ya ce mutanen mazaɓarsa ne suka buƙace shi da ya tsaya domin yi musu hidima.

“Ba domin kaina nake yin wannan ba. Jama’a ne suka kira ni domin in yi musu hidima, kuma zan yi musu hidima,” in ji shi.

Buba na neman kayar da Sadiq Ango Abdullahi, wanda ya lashe kujerar a shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kafin daga bisani ya koma APC.

Abdullahi na neman sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki a yanzu.

ArewaKadunaTakaraZaben 2027
Comments (0)
Add Comment