Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ware Naira miliyan 265 domin tallafa wa maniyyata aikin Hajjin 2026 guda 3,620 da suka yi rajista ta Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan ranar Lahadi yayin taron koyar da aikin Hajji a aikace da aka gudanar a Kano, inda ya kuma gargaɗi maniyyatan da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin hukumomin Saudiyya yayin zaman su a ƙasa mai tsarki.
Gwamnan, wanda Mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar za ta bai wa kowane maniyyaci Riyal 200 na Saudiyya domin sauƙaƙa musu gudanar da ibadarsu.
Garo ya tunatar da maniyyatan Kano da su shirya zuƙatansu da rayuwarsu domin tafiyar ibadar, yana mai cewa aikin Hajji na buƙatar haƙuri, ladabi da cikakkiyar biyayya wajen gudanar da ibadun da ake yi a Saudiyya.
Ya bayyana cewa taron koyarwar aikin Hajji a aikace na taimakawa maniyyata wajen fahimtar mataki-mataki na yadda ake gudanar da ibadun Hajji domin su gudanar da ibadarsu yadda ya kamata.
Mataimakin gwamnan ya buƙaci maniyyatan da su yi amfani da lokacin da za su shafe a ƙasa mai tsarki wajen ibada, neman gafara da kuma yi wa Najeriya da Jihar Kano addu’ar zaman lafiya da ci gaba.
A cewarsa, “Tafiyarku zuwa Saudiyya ba tafiya ta yau da kullum ba ce. Tafiya ce da ke buƙatar ilimi, ladabi, haƙuri da kuma cikakkiyar biyayya ga Allah domin gudanar da ibada yadda Musulunci ya tanada.”
Ya ƙara da cewa horon da ake bai wa maniyyatan zai taimaka musu wajen gudanar da aikin Hajji cikin tsari, aminci da cikakkiyar fahimtar muhimmancin ibadar.
Garo ya kuma yabawa shugabanci da ma’aikatan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano bisa ƙoƙarin da suke yi wajen shirya aikin Hajjin bana.
Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya ce an kammala duk shirye-shiryen tashin jirgin farko na maniyyatan da aka tsara ranar 14 ga Mayun 2026.
Matawalle ya ce an samar wa dukkan maniyyata da jami’an da za su raka su biza, tare da kammala allurar rigakafi da rabon kaya da jakunkuna kafin tafiyar.
Ya kuma gargaɗi maniyyata da su guji ɗaukar kayan da aka haramta a cikin kayansu tare da bin jadawalin jirage yadda aka tsara.
Matawalle ya ce an kuma shirya rabon kuɗin alawus na tafiya wato Basic Travel Allowance (BTA) ga maniyyatan.
Shi ma Kodinetan Shiyyar Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) mai kula da jihohin Kano, Kaduna da Katsina, Umar Muhammad, ya gargaɗi maniyyatan da su guji duk wani abu da zai zubar da mutuncin Kano da Najeriya a Saudiyya.
Ya kuma buƙace su da su kula da canjin kuɗi a Saudiyya tare da yin hattara da masu damfara da ka iya ƙwace musu kuɗaɗen BTA.
Daga cikin abubuwan da aka gudanar a taron akwai koyar da yadda ake gudanar da muhimman ibadun Hajji a Makkah, Mina, Arafat, Muzdalifah da Jamrat.