Mutum biyu sun rasa rayukansu bayan da wasu fusatattun mutane sukai musu dukan tsiya har suka mutu a ƙauyen Bunga da ke Ƙaramar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi bisa zargin sata da aka ce ba gaskiya ba ne.
Waɗanda aka kashe sun haɗa da Kabiru Idris mai shekara 30 da Ibrahim Danliti mai shekara 40, dukkaninsu mazauna ƙauyen Gabanga da ke Ƙaramar Hukumar Warji.
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Bauchi ta ce lamarin ya faru ne ranar 7 ga watan Mayun 2026 bayan samun kiran gaggawa kan harin da aka kai a ƙauyen Bunga da ke mazaɓar Dagu.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Nafiu Habib, ya fitar ranar Juma’a da dare, ya ce wasu mutane daga Ƙaramar Hukumar Ningi ne suka fara bin mutanen suna ihu da kiran “ɓarayi, ɓarayi”, lamarin da ya sa suka yi yunƙurin tserewa kafin a tare su.
“Mutanen suna tafiya ne a kan babur lokacin da wasu fusatattun mutane daga Ningi suka fara binsu suna kiran su ɓarayi har zuwa lokacin da aka tare su a ƙauyen Bunga inda aka yi musu mummunan duka har suka suma,” in ji Habib.
Ya ƙara da cewa jami’an ƴan sanda sun garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa Babban Asibitin Warji, inda likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Bayan faruwar lamarin, jami’an binciken rundunar sun kama mutum uku da ake zargi da hannu a harin bayan samun bayanan sirri.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Samaila Turawa na unguwar Gwada, Danbaba Haruna na Gwada, da Ubale Mai Kaji na Ningi.
Rundunar ta ce ana tsare da waɗanda ake zargin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar yayin da suke taimakawa bincike, tare da ci gaba da neman sauran mutanen da suka tsere bayan harin.