Majalisar Dattawa Ta Amince Da Gyaran Dokar Zaɓe Don Hana Rikice-Rikicen Shari’ar Kafin Zaɓe

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin gyaran Dokar Zaɓe ta 2026 da ke neman fayyace hurumin kotuna a shari’o’in kafin zaɓe tare da kawo ƙarshen saɓanin hukunce-hukunce da ke tasowa daga rikice-rikicen tsayar da ƴan takara.

Ƙudirin, wanda Sanata Simon Lalong mai wakiltar Plateau ta Kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin zaɓe ya ɗauki nauyi, ya tsallake karatu na biyu da na uku a ranar Alhamis.

TheCable ta rawaito cewa ƙudirin na neman kawo ƙarshen abin da ake kira “forum shopping”, wato yadda masu ƙara ke kai shari’a kotuna daban-daban a jihohi daban domin neman hukuncin da zai yi musu amfani a rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyu.

Sabon gyaran dokar ya ware takamaiman kotunan da za su riƙa sauraron shari’o’in kafin zaɓe domin hana fitowar hukunce-hukunce masu karo da juna daga kotuna masu matsayi iri ɗaya.

Haka kuma ƙudirin na neman tabbatar da cewa an warware rikice-rikicen fidda gwani kafin gudanar da babban zaɓe.

Ƴan majalisar sun bayyana cewa gyaran zai taimaka wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wajen kammala fitar da jerin ƴan takara cikin lokaci tare da samar da kwanciyar hankali ga shirye-shiryen zaɓe.

Wannan shi ne babban gyara na farko da aka yi wa Dokar Zaɓe ta 2026 wadda Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 18 ga Fabrairu.

Yayin muhawara kan ƙudirin, Simon Lalong ya ce demokaraɗiyya ba ta dogara da gudanar da zaɓe kaɗai ba, har ma da inganci da tabbas na tsarin shari’ar da ke gabatar da zaɓe.

“Idan tsarin shari’ar da ke kula da rikice-rikicen kafin zaɓe ya kasance mai cike da rashin tabbas ko saɓani, to tsarin zaɓe gaba ɗaya zai faɗa cikin ruɗani da jinkiri,” in ji shi.

Lalong ya ce ƙudirin na neman yin gyara ga sashe na 29 na Dokar Zaɓe tare da ƙara sabon sashe na 29A domin fayyace hurumin kotuna a irin waɗannan shari’o’i.

Ya bayyana cewa gyaran sashe na 29(5) zai bai wa masu neman takara damar shigar da ƙara ko dai a Babban Birnin Tarayya Abuja ko kuma a yankin da rikicin ya faru.

A cewarsa, sabon sashe na 29A zai tanadi cewa dukkan shari’o’in kafin zaɓe da suka shafi zaɓen sanatoci, gwamnoni da ƴan majalisar jihohi za su fara ne a babbar kotun tarayya, sannan ɗaukaka ƙara ta tafi kotun ɗaukaka ƙara.

Ya ƙara da cewa shari’o’in da suka shafi zaɓen shugaban ƙasa da mataimakinsa za su fara ne a kotun ɗaukaka ƙara kafin daga bisani a ɗaukaka su zuwa kotun ƙoli.

Lalong ya ce ƙudirin zai kawo ƙarshen “mummunar ɗabi’ar” shigar da ƙararraki iri ɗaya a kotuna daban-daban domin neman hukunci mai daɗi ga masu ƙara.

Sanata Mohammed Monguno mai wakiltar Borno ta Arewa kuma babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa ya goyi bayan ƙudirin, yana mai cewa zai taimaka wajen daƙile cin zarafin tsarin shari’a a harkokin zaɓe.

Shi ma Sanata Ekong Sampson mai wakiltar Akwa Ibom ta Kudu ya ce ɗabi’ar “forum shopping” na da hatsari ga demokaraɗiyya da tsarin siyasar ƙasa.

Sanata Adams Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce ƙudirin ba ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya kuma zai taimaka wajen rage doguwar taƙaddama kan tsayar da ƴan takara.

Tun da farko a ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta amince da ƙudirin.

DattawaNajeriyaShari'aZaben 2027
Comments (0)
Add Comment