Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya shiga takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Mohammed ya karɓi fom ɗin takara a ranar Alhamis a Abuja jim kaɗan bayan halartar taronsa na farko na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APM.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Yusuf Dantalle, ne ya jagoranci taron tare da sauran manyan shugabannin jam’iyyar.
Da yake jawabi yayin taron, Bala Mohammed ya soki abin da ya kira rashin bin ƙa’idojin demokaraɗiyya da tsoratar da ƴan siyasa a Najeriya, yana mai cewa hakan ya sanya siyasa ta zama mai wahala ga masu ra’ayin kawo sauyi.
Ya ce APM na da aƙidu irin nasa musamman a ɓangarorin shugabanci nagari, demokaraɗiyyar cikin gida, adalci, haɗa kai da mutunta doka, lamarin da ya sa ya yanke shawarar shiga jam’iyyar.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa wasu fitattun ƴan siyasa daga jam’iyyar PDP sun bi shi zuwa APM, ciki har da ƴan majalisar dokoki ta ƙasa, ƴan majalisar dokokin Bauchi, shugabannin ƙananan hukumomi, kwamishinoni, shugabannin mazaɓu da sauran magoya baya.
Ya ce matakin ba sauya sheƙa na mutum daya ba ne, illa wata gagarumar tafiyar siyasa da ke da nufin ƙarfafa APM da faɗaɗa tasirinta a faɗin ƙasar nan.
Matakin Bala Mohammed na neman kujerar majalisar dattawa ya zo ne kwanaki kaɗan bayan ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya ce yana neman kyakkyawar makoma ga mutanensa.
Kafin ficewarsa daga PDP, Mohammed shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar.
A baya, Bala Mohammed ya wakilci Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa bayan lashe zaben shekarar 2007 ƙarƙashin jam’iyyar ANPP.
Daga bisani aka naɗa shi Ministan Babban Birnin Tarayya a shekarar 2010 kafin ya koma jam’iyyar PDP.